Wani makeken dutse zai wuce kusa da duniya

Makeken dutse
Image caption Dutse zai wuce kusa da duniya

Wani makeken dutse mai girman kusan filin kwallo zai wuce ta kusa kusa da duniya a cikin yan sa'o'i masu zuwa.

Dutsen -- mai fadin murabba'in mita 45, ana sa ran zai kusanci duniya da kusan nisan kilomita dubu 28 -- kurkusa fiye da tauraran dan adam da kuma masu nazartar yanayi.

Masana ilmin kimiya sun ce babu hadarin cewar dutsen na Asteroid zai fado kan doron duniya, kuma ba shi da wata nasaba kwata kwata da mulmulen dutsen Meteor na Rasha .

Wata masaniyar kimiya a Jami'ar koyo daga gida a Milton Keynes, Farfesa Monica Grady ta ce lamuran biyu ba su da nasaba da juna.