Venezuela ta saki hoton farko na Shugaba Chavez

Chavez da yaransa biyu
Image caption Ana ci gaba da cece kuce akan lafiyar Chavez

Gwamnatin Venezuela ta saki hoton farko na Shugaba Hugo Chavez tun lokacin da akai masa aikin ntiyata a karo na hudu game da cutar daji da yake fama da ita, a Kasar Cuba cikin watan Disambar bara

Hoton dai na nuna Mr Chavez yana murmushi a kwance tare da yaransa mata biyu a gefen sa.

Gwamnatin Venezuelan ta saki karin bayanai game da halinda yake ciki

Ministan yada labaru Ernesto Villegas yace Shugaba Chavez yana numfashi ne ta hanyar bututu a cikin makwogaran sa, kuma yana shan wahala wajen yin magana

Karin bayani