Harbin bindiga ne ajalin Dorner —jami'ai

Christopher Dorner
Image caption Christopher Dorner tsohon dan sanda ne kuma tsohon sojan ruwa

Jami'ai a Jihar California ta Amurka sun ce dan sandan nan da aka yi ta farautarsa wanda aka samu gawarsa a kone a tsaunukan Los Angeles ya mutu ne sakamakon raunin da ya yi a ka.

Wani binciken da likitoci suka gudanar a kan gawar Christopher Dorner ya nuna cewa raunin da ya yi a ka sakamakon wani harbi daya na bindiga ne ya yi ajalinsa.

Sai dai kuma babban jami'in 'yan sanda na yankin San Bernadino, wanda ya bayar da sanarwar sakamakon binciken yayin wani taron manema labarai, ya ce ba a iya tantancewa ba ko Dorner ne ya habe kansa ko harbe shi aka yi.

A makon da ya gabata ne dai tsohon jami'in dan sandan na birnin Los Angeles ya ranta a na kare bayan an zarge shi da kisan mutane uku—ciki har da dan sanda daya—da kuma jikkata wasu mutanen uku.

Wani dan sandan kuma ya rasa ransa kafin gobara ta tashi ta kuma kone dakin da Dorner ya buya a tsaunukan Los Angels.

Dorner ya wallafa wata sanarwa mai daga hankali a shafinsa na Facebook wadda a ciki ya yi barazanar zai kashe wadansu ’yan sanda da iyalansu, ya kuma zargi Rundunar ’Yan Sanda ta Los Angeles da korarsa daga aiki ba bisa ka'ida ba a shekarar 2008.

Ranar Talata farautar da ake yi ta tsohon dan sandan ta kawo karshe bayan kwanaki shida.

Karin bayani