Ministocin kasashe 20 za su gana a Moscow

Shugabannin kasashen G20
Image caption Kasashen G20 na yunkurin yiwa ka'idojin haraji kwaskwarima

Ministocin kudi daga kasashen duniya ashirin masu karfin tattalin arziki, wato G20, za su gana a Moscow.

Yayin ganawar, ministocin za su tattauna a kan wani yunkuri na yin kwaskwarima ga ka'idojin biyan haraji wadanda ke baiwa manyan kamfanoni damar kaucewa biyan harajin.

Birtaniya, da Jamus, da Faransa ne ke jagorantar yunkurin na daukar matakin ba-sani-ba-sabo a kan manyan kamfanonin kasa-da-kasa masu kaucewa biyan haraji ta hanyar karkatar da ribar da suke samu zuwa kasashen da suke da hedkwata, inda ake yi musu rangwamen haraji.

Yunkurin dai na zuwa ne yayin da muhawara ta yi zafi a Birtaniya bayan ta bayyana cewa manyan kamfanoni irinsu Google, da Amazon, da Starbucks na biyan harajin da bai taka kara ya karya ba idan aka kawatanta da dimbin kudin shigar da suke samu a kasar ta Birtaniya.

Karin bayani