Bam ya tashi a Jihar Bornon Najeriya

Babban Hafsan Dakarun Tsaron Najeriya, Admiral Ola Ibrahim
Image caption Babban Hafsan Dakarun Tsaron Najeriya, Admiral Ola Ibrahim

Wani bam ya tashi da yammacin jiya lokacin da wadansu maharan suka tunkari motocin sunturi na jami'an tsaro na Rudundunar Hadin Gwiwa ta JTF a kasuwar Gambaru, daura da babbar hanyar zuwa Gamboru-Ngala a Jihar Borno da ke arewacin Najeriya.

A wata sanarwa da ta fitar, rundunar ta JTF ta tabbatar da faruwar al'amarin, tana mai cewa sanadiyar fashewar bam din wuta ta watsu ta kona gidaje da shagunan da ke kewaye da wajen.

A sanarwar mai dauke da sa hannun kakakinta, Laftanar Kanar Sagir Musa, rundunar ta ce mutane biyu—wadanda ake zargin maharan ne—da wani soja daya sun rasa rayukansu.

Ta kuma ce bam din ya yi kaca-kaca da wata motar rundunar ta JTF, ko da yake babu wani farar hula da abin ya shafa.

Karin bayani