Kungiyar agaji ta Red Cross ta shekara 150

Tambarin Red Cross
Image caption Kungiyar agaji ta Red Cross ta shekara 150

Ranar Lahadi kungiyar agaji ta kasa-da-kasa ta Red Cross (ICRC) ke bikin cika shekara dari da hamsin da kafuwa—ita ce dai kungiya mafi dadewa a duniya.

An kafa kungiyar ne a shekarar 1863 da nufin taimakawa wadanda suka jikkata a yakin Solferino—yakin da aka fafata tsakanin Faransa da Austria a 1859.

Wani dan kasuwa mutumin Geneva Henri Dunant ne ya kafa ta.

Yanzu haka kungiyar ta ICRC na gudanar da ayyukanta a wurare da dama da ake fama da rikice-rikice a duniya, sai dai ta ce kalubalen yake-yaken zamani na kara sanya ayyukan nata suna wahala.

Wakiliyar BBC a Geneva ta ce ko da yake ana martaba kungiyar ta ICRC, ba ta cika goma ba—shawarar da ta yanke ta jan bakinta ta yi shiru dangane da sansanonin gwale-gwale na ’yan Nazi ta jawo mata kakkausar suka—daga karshe sai da ta nemi afuwa.

Karin bayani