Dan kunar bakin wake ya kashe mutane sittin a Pakistan

Wurin da aka kai hari a Quetta na Pakistan
Image caption Wurin da aka kai hari a Quetta na Pakistan

Yansanda a Pakistan sunce mutane akalla 60 ne aka kashe a wani harin bam a birnin Quetta dake kudu maso yammacin kasar.

Wani Kakakin yansanda ya ce, kusan wasu mutanen 200 ne kuma suka samu raunuka a lokacin da bam din ya tashi a wani buki da cike da jama'a.

Wata kungiyar masu tsatstsauran ra'ayi ta yan Sunni Lashkar -e- Jhangvi ta ce ita ce keda alhakin kai harin bam din.

Galibin wadanda abun ya shafa dai --da suka hada da mata da kananan yara -- yan Shi'ar Pakistan ne tsirarru wadanda kungiyoyin yan gwagwarmayar yan Sunni masu tsatstsauran ra'ayi ke ta kai wa hari.

Karin bayani