An harbi wani dan jarida a Sri Lanka

Faraz Shauketaly, dan jaridar da aka harba a Sri Lanka
Image caption Faraz Shauketaly, dan jaridar da aka harba a Sri Lanka

An harbe wani danjaridar dake bankado ababuwa a Srilanka, aka kuma jikkata shi sosai a gidansa dake a kusa da Colombo, babban birnin kasar.

An yiwa Danjaridar, Faraz Shauketaly wanda ke aiki da wata jaridar dake fitowa ranar lahadi, aikin tiyata, kuma an ce baya a cikin hadari.

Jaridar Mr Shauketaly, mai suna The Sunday Leader, tana sukar gwamnati , kuma ya bayyana damuwa cewar rahotanninsa na bankado ababuwa za su iya saka rayuwarsa cikin hadari.

Shekaru huda da suka wuce an harbe Editan Jaridar ta ranar lahadi har kahira.

Karin bayani