Firayim Ministan Tunisia yayi murabus

Shugaba Marzouki na Tunisia
Image caption Shugaba Marzouki na Tunisia

Firayim ministan kasar Tunisia Hamad Jebali, ya bayar da sanarwar yin murabus daga kan mukaminsa a wani jawabi da ya yiwa jama'ar kasar kai tsaye ta gidan talabijin, bayan ganawar da ya yi da shugaban kasar Moncef Marzouki.

Ya kuma ce ba zai tsaya takara a zaben da za a yi nan gaba ba.

Hakan dai ya faru ne bayan da jam'iyyarsa ta Ennahda ta yi watsi da shirinsa na kafa gwamnatin kwararru domin kaucewa rikici a kasar.

Hakan dai ya biyo bayan kisan gillar da aka yi wa wani jagoran adawa ya haifar da gagarumin sabani tsakanin masu goyon addinin musulunci da kuma wadanda basu damu da addinin ba.