David Cameron na ziyara a India

David Cameron a India
Image caption Firayim Minista David Cameron na Burtaniya ya sauka a India

Firayim Ministan Burtaniya David Cameron ya sauka a India, inda zai jagoranci wani yunkuri na biyu na habaka cinikayya bayan wata ziyara da ya kai a shekarar 2010.

Mista Cameron na jagorantar wata babbar tawaga ta ’yan kasuwar Burtaniya wadanda za su duba hanyoyin cin moriyar tattalin arzikin kasar India wanda shi ne na biyu a duniya wajen bunkasa cikin hanzari.

Ita ma kasar ta India yanzu ta zama babbar mai zuba jari a Burtaniya.

India dai na cikin kasashen da David Cameron ya fara kaiwa ziyara jim kadan bayan ya zama Firayim Minista a shekarar 2010.

Kafin ziyarar tasa ya ce yana so dangantakar Burtaniya da India ta zama daya daga cikin manya-manyan kawancen karni na ashirin da daya. Yana kuma fata kamfanonin Burtaniya za su samu muhimman kwangiloli a kasar ta India.

Mista Cameron na kuma zawarcin karin daliban India su je su yi karatu a jami'o'in Burtaniya, amma kuma Indiyawa da dama na ganin hakan ba zai yiwu ba saboda tsauraran ka’idojin bayar da izinin shiga kasar wato visa.

Sai dai kuma Mista Cameron zai yi kokarin kawar da wannan fargaba: kafin fara ziyarar tasa ya ce ba za a kayyade adadin dalibai ’yan India da za su iya zuwa Burtaniya karatu ba.

Firayim Ministan yana kuma fatan zai iya gamsar da jama’a cewa Burtaniya ta fi ko wacce kasa dacewa da cinikayya da India.

Karin bayani