Rafael Correa ya lashe zabe karo na uku

Shugaba Rafael Correa
Image caption Shugaba Rafael Correa ya yi jawabin godiya ga magoya bayansa a kusa da fadar shugaban kasa

Sakamakon farko-farko na zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar Lahadi a Ecuador ya nuna cewa Shugaba Rafael Correa ya yi nasarar samun damar ci gaba da rike mukaminsa.

Adadin kuri’un da dama aka yi hasashen shugaban kasar mai ra’ayin gurguzu zai samu ya kai yadda ba sai an je zagaye na biyu ba kuma tuni ma dai abokan hamayyarsa suka amince da shan kaye.

Wannan wa’adi na uku da masu zabe a Ecuador suka baiwa Shugaba Correa dai zai ba shi damar kara kankame madafun iko a kasar mai arzikin man fetur, ya kuma kara tagomashin kawancen shugabannin kasashen Latin Amurka masu ra’ayin gurguzu.

Sakamakon farko da hukumar zabe ta kasar ta fitar ya nuna cewa Rafael Correa ya lashe kashi hamsin da takwas cikin dari na kuri’un da aka riga aka kidaya yayin da dan takarar da ke bi masa, Guillermo Lasso, ya samu kashi ashirin da hudu cikin dari.

Da yake jawabi ga dimbin magoya bayansa—wadanda suka taru a kusa da fadar shugaban kasa dake Quito, babban birnin kasar—Mista Correa ya ce:

“Ina godiya da kwarin gwiwar da kuka nuna a shugabanci na. Kun san cewa ba mu taba ba ku kunya ba, kuma ba za mu ba ku kunya ba.

“Wannan nasara taku ce—nasara ce ga iyalanmu, da ’ya’yanmu, da abokanmu, da makwabtanmu, da ma kasarmu baki daya”.

Tun a shekarar 2007 ne dai Mista Correa ya dare karagar mulkin kasar, sannan ya yi amfani da arzikin man da Allah Ya huwace mata wajen gina hanyoyin mota, da asibitoci, da makarantu a yankunan karkara da unguwannin marasa galihu—abin da ya jawo masa farin jini sosai a wajen talakawa.

Sai dai kuma masu sukar lamirinsa na zargin Mista Correa da yin babakere a kan al’amuran kasar.

Masharhanta dai na ganin zaben wata dama ce ga Mista Correa ya gaje jagorancin kawancen shugabannin yankin masu adawa da Amurka, kasancewar an daina jin duriyar Shugaba Hugo Chavez na Venezuela, wanda ke fama da cutar cancer.

Karin bayani