Afghanistan: Farar hula da ke mutuwa na raguwa

Hamid Karzai
Image caption Shugaba Hamid Karzai ya ce zai haramtawa sojojin Afghanistan neman dauki daga sojin sama na NATO

Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya nuna cewa a karo na farko a cikin shekaru shida yawan fararen hular da tashe-tashen hankulan Afghanistan ke rutsawa da su ya ragu.

Sai dai kuma ko da yake adadin daukacin fararen hular da al’amarin ke shafa ya ragu a shekarar 2012, adadin wadanda ke jikkata ya dan karu.

Raguwar fararen hular da ke mutuwa da kashi goma sha biyu cikin dari dai na nuni da cewa Afghanistan ta kama hanyar zama wani wuri da mutanen da ba mayaka ba ne ke da aminci.

Rahoton, wanda Hukumar Agazawa Afghansitan ta Majalisar Dinkin Duniya ta wallafa, ya nuna cewa masu tayar da kayar baya ne suka haddasa mutuwar ko raunata kashi tamanin cikin dari na wadanda tashe-tashen hankulan kan shafa, kuma yawan kisan gillar da kungiyar Taliban ke aikatawa ya karu matuka.

Mutuwar fararen hula dai al'amari ne mai sarkakiya a siyasar Afghanistan; kuma yawan fararen hular da ke mutuwa sakamakon ayyukan rundunar kungiyar tsaro ta NATO da dakarun Afghanistan ya ragu sosai.

Wannan labari dai mai dadin ji ne ga dakarun kasashen waje, wadanda ke fuskantar matsin lamba daga gwamnati a makon da ya gabata a kan su takaita kai hare-hare da jiragen saman yaki a yankunan da fararen hula ke zaune.

Karin bayani