Chavez ya koma Venezuela

Image caption Masu goyon bayan Chavez suna murnar komawarsa gida

Shugaban ƙasar Venezuela Hugo Chavez ya sanar a shafinsa na Twitter cewa ya koma gida daga jinyar da yake yi a ƙasar Cuba.

Da yake magana kafin fitar da sanarwar, mataimakin shuagaban kasa Nicolas Maduro ya ce, masu adawa da Mr Chavez a kafafen yada labarai ba sa so ya warke.

Shugaba Chavez ya kuma ce, wadanda suka mallaki kafafen yada labarai na da da kuma na yanzu, sun bayyana kiyayya matuka ga shugabanmu, kuma suna wasa da rayuwa.

Mr Chavez ya je Cuba ne domin yi masa maganin cutar Dajin da ke damunsa.

Wannan ita ce jinya ta hudu da ya kwanta a cikin watanni takwas.