Ba hari aka kai ba a Legas! Inji 'Yan sanda

A Najeriya rundunar 'yan sanda a jahar Lagos ta tabbatar da mutuwar mutum guda yayin da wani kuma ya samu raunuka, bayan da wani abu ya fashe a unguwar FESTAC, dazu da rana.

Wasu rahotanni dai sun ce bam ne ya tashi a kusa da wata gada a unguwar to amma kwamishinan 'yan sandan jahar, Umar Manko wanda ya tabbatarwa manema labarai afkuwar lamarin ya musanta hakan inda ya ce jami'ansu na gudanar da bincike game da musabbabin fashewar.

Wannan dai na zuwa yayin da matsalar tsaro a Najeriya ke ci gaba da tabarbarewa.