'Yan PDP na son shiga APC —Shekarau

Malam Ibrahim Shekarau
Image caption Tsohon Gwamnan Jihar Kano ta arewacin Najeriya, Malam Ibrahim Shekarau

Tsohon Gwamnan Jihar Kano a arewacin Najeriya, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce wadansu manyan jami’an jam’iyyar PDP mai mulkin kasar sun fara nuna sha’awar shiga sabuwar jam’iyyar APC.

A cewarsa, “A daidaku, ba gwamnoni na PDP kawai ba, akwai wasu daga cikin jami’ai ko ’ya’yan jam’iyyar PDP wadanda suka fara tuntubar mu [da] cewa suna da sha’awa su shigo cikin wannan tsari, kuma muka ce kofar mu a bude take”.

Sai dai kuma, tsohon gwamnan ya ce yana ganin da dama daga cikinsu za su jira su ga “ta gama nuna” kafin su bayyana abin da ke zukatansu.

Mai baiwa shugaban kasa shawar kan harkokin siyasa, Ahmed Gulak ya ce, Shugaba Goodluck Jonathan nada masaniyar cewa wasu gwamnoni a kasar na yiwa PDP zagon kasa saboda su cimma bukatunsu.

Gulak a wata hira da yayi da wani gidan talabijin a kasar ya ce, gwamnonin ba za su yi narasa ba.

Shima Malam shekarau a wata hira da ya yi da BBC, lokacin da ya kai ziyara ofishinmu da ke London, ya ce suna sane da rahotannin da ke cewa ana kokarin amfani da wadansu bara-gurbi domin kawo tsaiko a tafiyar ’yan adawar.

“Mun ga wadannan zarge-zarge a kafafen yada labarai, kuma mun kirawo wadanda wannan zargi ya fada kansu sun tabbatar mana cewa babu gaskiya, wannan yarfe ne na siyasa…”.

*Masu saurare za su iya jin cikakkiyar hirar ranar Asabar 23 ga wata a filinmu na Gane Mani Hanya a Shirinmu na Safe wanda ke zuwa da karfe shida da rabi agogon Najeriya da Nijar a kan mita 25, da 41 da kuma 49.

Karin bayani