An sace wasu Faransawa bakwai a Kamaru

Taswirar Kamaru
Image caption Kasar Kamaru ta hada iyaka da Najeriya

Rahotanni daga Kamaru sun ce an yi garkuwa da wasu 'yan kasar Faransa akalla bakwai, a arewacin kasar kusa da kan iyaka da Najeriya.

An kame mutanen ne a wani kauye dake kimanin kilomita 10 daga Najeriya.

Jami'an tsaro a Kamaru sun ce sun yi amanna cewa, mutanen na komowa ne daga wajen shakatawa na Waza, inda 'yan kasashen waje ke zuwa yawon bude ido.

An ambato ofisihin jakadancin Faransa a Yaounde na cewa, wasu yan bindiga ne a kan babura suka kame mutanen, inda suka nufi Najeriya da su.

Shugaban kasar Faransa Francios Hollande ya ce iyali guda aka sace, kuma akwai yara hudu a cikinsu.

Inda ya kara da cewa kungiyar masu fafutuka a Najeriya ce ta yi awon gaba da Faransawan, kuma hukumomin Faransa sun san kungiyar.

Hakan na zuwa ne a lokacin da Faransa ke jagorantar yaki da masu fafutukar Islama a Mali.