David Cameron ya kafa tarihi

Image caption David Cameron

David Cameron ya zama Firai Ministan Birtaniya na farko da ya ziyarci wajen da sojojin Birtaniya na zamanin mulkin mallaka suka aiwatar da kisan kiyashi a India, kusan shekaru dari da suka wuce.

A ranar karshe ta ziyarar da ya kai India, Mista Cameron ya ajiye fure na girmamawa a wajen domin girmamawa da kuma tunawa da daruruwan mutanen da aka kashe a shekarar 1919.

Dakarun mulkin mallaka a Amristar da ke Punjab ne a wancan lokacin suka bude wuta a kan mutanen da ba sa dauke da wani makami ba tare da wani gargadi ba.

Mista Cameron bayyana lamarin a matsayin wani abin kunya a tarihin Burtaniya.

A cewar Mista Cameron bai kamata a manta da lamarin da ya faru ba.

Kodayake Mista Cameron bai nemi afuwa game da kisan kiyashin ba, amma kalamansa sun nuna yadda Birtaniya take matukar takaicin kisan.

Karin bayani