Shugaban Alkalan Kenya na fuskantar barazana

Kenya
Image caption Ana shirin zabe a Kenya

Shugaban alkalan kasar Kenya ya ce yana fuskantar barazana gabanin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun kasar da za a yi a watan gobe.

A wata sanarwa da ya aikewa manema labarai, babban mai shari'a Willy Mutunga, ya ce ya samu sakon barazana a wata wasika da kungiyar 'yan daba ta Mungiki ta aike masa.

Ya ce wasikar ta gargade shi kan kada ya haramtawa da daya daga cikin 'yan takarar shugaban kasar Uhuru Kenyatta, shiga zaben na watan gobe.

Wakilin BBC ya ce ana yiwa Alkalin Alkalan kallon wani mutum da ke kokarin kawo sauyi a fannin shari'ar kasar - wanda ke cike da cin hanci da rashawa. Kuma za su taka rawa sosai a zaben na watan gobe.

A makon da ya gabata ma yayi korafin cewa wani jami'in shige da fice, ya yi kokarin hana shi hawa jirgi domin fita kasar waje, har sai ya nemi izini daga shugaban shugaban ma'aikatan kasar.

Karin bayani