'An ji ihu da harbi a gidan Pistorius'

Oscar Pistorius
Image caption Mr. Pistorius ya ce a lokacin da ya yi harbi ya dauka barawo ne ya shiga gidansa

Wani mai bada shaida a shari'ar da ake game da zargin kisan da ake wa Oscar Pistorius, ya ce ya ji ihu da harbe-harbe a gidan dan wasan.

Jami'in dan sandan da ya bayyana hakan, ya ce hakan ya faru ne a daren da aka kashe Reeva Steenkamp.

A rana ta biyu na shari'ar da ake yi a Pretoria, game da bada belin Mr. Pistorius, dan sandan ya ce zakaran wasan zai iya tsere wa.

Shi dai Oscar ya musanta zargin da ake masa na kisan Reeva da gangan.

Masu gabatar da karar sun kuma ce, an ji ana fada a gidan Oscar da misalin karfe biyu zuwa uku na daren da lamarin ya auku.

Jami'in dan sandan da ya fara isa gidan Oscar, Mr Botha ya ce suna da rahoton dan sanda , wanda wani shaida yace ya ji muryar mace tana ta ihu sannan kuma ya ji harbi fiye da sau daya daga gidan Mr. Pistorius.

Sai dai Mr. Pistorius ya ce basu yi fada da Reeva ba, kuma ya yi barci har kusan gaf da lokacin da aka ji harbin.

Karin bayani