'Yan Afirka miliyan 210 ba su da tsaftataccen muhalli'

Image caption Wata yarinya za ta je debo ruwa

Wani rahoto da kungiyar Water Aid, mai yunkurin ganin an samar da tsaftataccen ruwa ta fitar ranar Laraba, ya ce kimanin 'yan Afrika miliyan 210 ne ke fama da rashin tsaftar muhalli sakamakon karancin ruwa.

Sabon rahoton ya ce gwamnatocin Afrika sun gaza cika alkawuran da suka dauka na samar da kudade domin tsaftar muhalli.

Water Aid ta gudanar da bincike a kasashen Ghana da Nijar da Saliyo da Uganda da kuma Rwanda.

Kazakila rahoton ya yi gargadin cewa matukar ba a kara kudade a bangaren samar da ruwa ba, to bunkasar birane da sauyin yanayi, da kuma karuwar jama'a za su yi sanadiyar fuskantar koma baya a harkar tsafta.

Karin bayani