Akalla mutane 8 sun halaka a Maiduguri

MD Abubakar, babban Spetan 'yan sandan Najeriya
Image caption Ana ci gaba da samun asarar rayuka a birnin Maiduguri

Rahotanni daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno na cewa, akalla mutane takwas ne su ka mutu sanadiyar fashewar wani abu da ake kyautata zaton bam ne a unguwar kwastan.

Bakin hayaki ya turnike sararin samania kamar yadda shaidun gani da iddo su ka tabbatar, tare da cewa Shaguna da dama da su ka kone.

Wasu magidanta a Maidugurin sun tabbatar wa da BBC cewa sun ga gawawwakin mutane a kwance.

Wannan al'amari dai ya kara janyo zaman zulumi a birnin.

Ko a ranar laraba ma dai, wasu mutane uku sun mutu bayan fashewar wani abu a birnin Maidugurin.

Karin bayani