Shari'ar Pistorius: An nada sabon jami'in dan sanda

Pistorius
Image caption Pistorius

An sauya jami'in dan sandan da ke jagorantar binciken kisan kan da ake zargin Oscar Pistorius da shi, bayan da ta bayyana cewar shi kansa ya na fuskantar tuhume-tuhume bakwai na kokarin aikata kisan kai, shekaru biyun da suka wuce.

Kwamishinar 'yan sanda ta kasa a Afrika ta Kudu, Mangwashi Victoria Phiyega ce ta bayar da sanarwar inda tace 'Na yanke shawarar wannan muhimmin batu , wannan muhimmin bincike a karkashin shugabanci da jagorancin Kwamishin gunduma kan ayyukan bincike, Lt Janar Moonoo'.

Shi dai dan tseren, Oscar Pistorius, ana zarginsa ne da kashe budurwarsa, Reeva Steenkamp.

A gobe Juma'a, ake sa ran za a yanke hukunci game da shari'ar neman belin da aka shigar kan Mr Pistorius.

Karin bayani