'An kashe mutane tara a Filato'

Image caption 'Yan sandan Najeriya

Rahotanni daga jihar Filaton Najeriya na cewa 'yan bindiga da a ba san ko su wanene ba sun kashe mutane tara a harin da suka kai a yankin Vom a ranar Alhamis da daddare.

Sai dai kwamishinan 'yan sandan jihar, Mista Chris Olakpe, ya shaidawa BBC cewa gawarwakin mutane hudu suka gano.

Jihar Filato dai ta dade tana fama da rikice-rikicen da suke da dangantaka da kabilanci da addini da kuma siyasa.

Karar harbe-harbe a Maiduguri

Rahotanni daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno, na cewa an shafe daren ranar Alhamis ana jin karar harbe-harben bindigogi a sassa daban-daban na birnin.

Sai dai har yanzu ba a san ko wannan lamari ya yi sanadiyar mutuwa ko jikkata mutane ba.

Ko a ranar Laraba ma , akalla mutane takwas ne suka mutu sanadiyar fashewar wani abu da ake zaton bam ne a unguwar Kwastan da ke birnin.

Haka kuma shaidu sun ce bakin hayaki ya turnike sararin samaniya, kuma shaguna da dama sun kone.

Karin bayani