Zanga zangar Bangaladesh: Mutum 4 sun mutu

Zanga Zangar Bangladesh
Image caption masu zanga zanga sun yi arangama da jami'an tsaro

'Yan sanda a Bangladesh sun ce a kalla mutane hudu sun rasa rayukansu daga cikin masu zanga zangar da su ka yi arangama da jami'an tsaro.

Dubban jama'a ne daga hadin gwiwar kungiyoyin addinin musulunci suka gudanar da zanga zanga a a Dhaka babban birnin kasar

Masu zanga zangar su na kiran zartar da hukuncin kisa akan masu shafukan internet na Blog wadanda su ka zarga da aikata mummunan sabo.

'Yan sanda sun yi amfani da harsasan roba da hayaki mai sa kwalla wajen tarwatsa an zanga zangar.

An yi makamancin arangamar a wasu sassa a fadin kasar.

Karin bayani