An samu karuwar cutar daji a wasu kauyukan China

Cutar cancer ko kuma daji
Image caption China na amfani da sinadarai masu guba ga jikin dan Adam

Ma'aikatar muhalli ta kasar China a karon farko ta amince da kasancewar wasu kauyuka inda gurbacewar muhalli ta haddasa yawaitar kamuwa da cutar Cancer.

Amincewar wadda ma'aikatar muhallin ta baiyana a cikin wani rahoto, ya zo a daidai lokacin da jama'a ke kara baiyana damuwarsu da kuma bacin rai a game da illar gurbtar iska da kuma dagwalon masan'antu, sakamakon bunkasar ayyukan ci gaban tattalin arziki.

Kafofin yada labarai sun ruwaito cewa yawaitar kamuwa da cutar Cancer ko kuma daji ga mazauna kauyukan dake kusa da masana'antu ya karu a yan shekarun nan.

A rahotan ta, ma'ikatar ta amince cewa China na amfani da sinadarai masu illa wadanda aka haramta amfani da su a Kasashe masu tasowa.

Karin bayani