Ba za mu biya diyya a Haiti ba — Ban Ki Moon

Image caption Ban Ki Moon

Majalisar Dinkin Duniya ta yi watsi da bukatar da 'yan kasar Haiti suka yi cewa ta ba su diyya bayan da suka kamu da cutar amai da gudawa.

Ana zargin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar da ke aiki a Haiti, da kai kwayoyin cutar amai da gudawa kasar, lamarin da ya sanya fiye da mutane 600, 000 suka kamu da ita.

Kimanin mutane 8000 sun mutu sakamakon lamarin tun daga shekarar 2010.

A wata sanarwa da kakakin Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, ya fitar ya ce wani kuduri da babban taron Majalisar ya amince da shi ya ba ta kariya daga biyan diyya ga 'yan kasar ta Haiti.

Majalisar ta ki amincewa da aikata laifi duk da cewa wadansu shaidu sun nuna ma'aikatanta ne 'yan asalin kasar Nepal suka yi sanadiyar barkewar cutar sakamakon zubar da sharar da su ka yi a wani kogi na kasar ta Haiti.

Wani lauyan mutanen ya shaidawa BBC cewa za su nufi babbar kotun kasar don ganin an tilastawa Majalisar biyan diyya.