Mun shiga matakin karshe a Mali —Hollande

Shugaba François Hollande na Faransa
Image caption Shugaba François Hollande na Faransa ya ce an shiga matakin karshe a yakin Mali

Shugaba François Hollande na Faransa ya ce dakarun kasarsa da ke jagorantar yakin da ake yi da masu tsattsauran ra'ayin Musulunci na kasar Mali sun shiga taki na karshe na fatattakar ’yan tawaye daga inda suke buya a kan wadansu tsaunuka.

Yayin wani taron manema labarai a birnin Paris, Mista Hollande ya jinjinawa dakarun sojin Chadi wadanda suka yaki ’yan tawayen a arewacin Mali.

“Ana fafatawa a arewacin Mali—na riga na shaidawa al’ummar Faransa cewa dakarun mu suna fafatawa kai tsaye da ’yan tawayen”, inji Mista Hollande.

Sojojin Chadi goma sha uku ne suka rasa rayukansu yayin wani artabu ranar Juma'a, yayin da mayakan ’yan tawaye sittin da shida suka rasa rayukansu.

Karin bayani