An kashe mutane biyar a Gombe

Image caption 'Yan sandan Najeriya

Rahotanni daga jahar Gomben Najeriya na cewa wasu 'yan bindiga a kan babur sun kashe mutane biyar da ke wasan karta a unguwar Bagadaza ranar Juma'a da yamma.

Ganau sun shaidawa BBC cewa mutane tara ne suka samu raunuka sakamakon harin.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Mohammed Sule, ya tabbatarwa BBC da aukuwar lamarin.

Ya kara da cewa sun kama wani mutum wanda suke zargi da hannu a kai harin.

Karin bayani