Iran zata kafa tashoshin makamashin nukiliya

Image caption Tashar nukiliya ta Bushehr a Iran

Gwamnatin Iran tace ta keɓe wurare goma sha shida da za'a gina tashoshin samar da makamashin nukiliya.

Ƙungiyar dake sa ido akan makashin nukiliya ta kasar ta kuma bayyana cewa, ta gano wuraren dake da dimbin makamashi Uranium da ma ya rubanya har sau uku yawan wanda aka yi tsammanin akwai a kasar.

Karkashin takunkumin majalisar dinkin duniya dai an haramtawa Iran fitar da duk wani abu da ya shafi nukiliya.

Masu lura da al'amura dai na cewa, wannan sanarwa da Iran tayi tana iya kawo karin sarkakiya akan tattaunawar da ake shirin yi a Kazakhstan ranar Talata akan wannan batu.