Amurka ta yi Allah-wadai da Syria

Victoria Nuland
Image caption Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Victoria Nuland

Amurka ta yi Allah-wadai da jerin hare-haren makami mai linzami da gwamnatin Syria ta kai a kan birnin Aleppo da ke arewacin kasar.

Mutnane da dama ne dai masu fafutuka suka bayar da rahoton cewa sun rasa rayukansu a hare-haren da aka kai a kan gundumar Tariq al-Bab ranar Juma'a.

A wata sanarwa mai dauke da sa-hannun mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Waje Victoria Nuland, gwamnatin Amurka ta yi amfani da kakkausan lafazi wajen yin Allah-wadai da hare-haren.

Sanarwar ta ce harin da aka kai ranar Juma'a da makami mai linzami samfurin Scud, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a gabashin birnin, ya biyo bayan wadansu hare-haren ne wadanda aka kai ranar Talata—wadanda suka ruguza gidajen kwanan jama'a suka kuma jikkata daruruwan fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba a gundumar Jabal Badr.

A cewar Amurka, wadannan hare-hare, da ma wadansu daban—ciki har da wanda aka kai a farkon makon jiya a kan wani asibitin jeka-na-yi-ka—alama ce ta irin rashin imani da rashin tausayin da gwamnatin Syria ke nunawa al’ummar da ta ke ikirarin wakilta.

Ma'aikatar Harkokin Wajen ta Amurka ta kuma ce gwamnatin Assad ba ta da halalci kuma tana ci gaba da mulki ne kawai ta hanyar amfani da karfin tuwo.

Sanarwar ta kara da cewa Amurka ba ta tsammanin mutanen Syria za su taba amincewa da shugabannin da hannayensu suka yi dumu-dumu da jinin talakawa a yunkurin nemawa kasar kyakkyawar makoma.

Wannan sanarwa dai ta zo ne bayan gamayyar kungiyoyin ’yan adawar Syria ta janye daga wadansu tarurrukan tattaunawa da za a yi a Washington, da Moscow da kuma Roma, don nuna rashin jin dadinta da abin da ta kira kame bakin da kasashen duniya suka yi dangane da hare-haren na makami mai linzami.

Mai magana da yawun ’yan adawar a London, Walid Saffour, ya shaidawa BBC cewa za su kauracewa tarurrukan ne don bayyana fushinsu ga kasashen na duniya:

“A gamayyar kungiyoyin ’yan adawa da ma Majalisar Kasa ta Syria mun fusata sosai da yadda kasashen duniya suka yi gum da bakinsu dangane da abin da ke faruwa a Syria, da haren-haren makami mai linzami samfurin Scud, wadanda suka ruguza biranen Aleppo da Hama da ma wadansu sassan Syria”.

A abin da ke nuna alama cewa Amurka ta yunkuro ne don daukar mataki a kan wannan korafi, sanarwar ta ce jami'ai a Washington na sa ran ganawa nan ba da jimawa ba da “halaltatun wakilan al'ummar Syria” don tattauna irin rawar da Amurka da sauran kawayenta za su taka wajen kawo sauyin da ake bukata a Syria.

Karin bayani