Fadar Vatican ta koka da kafofin yada labarai

Yayin da Paparoma Benedict ke shirin sauka daga mukaminsa, fadar Vatican ta maida martani da kakkausan lafazi dangane da abinda ta ce, wasu rahotanni a kafofin yada labarai dake da nufin matsa lamba ga manyan Limanan cocin da zasu zabi sabon Paparoma.

Babbar sakatariyar fadar Vatican din tace, duk da cewa a baya manyan kasashe sun yi kokarin yin katsa landan a zaben Paparoma, amma a wannan karon ana kokari ne ayi katsa-landan din ta hanyar jan ra'ayoyin jama'a.

Kakakin fadar ta Vatican, Father Federivo Lombardi ya kuma koka da cewa, akwai wasu dake kokarin zubar da kimar cocin ta hanyar amfani da yada gulma da cin fuska.

Wakilin BBC ya ce kakakin fadar ta Vatican ya kuma zargi kafofin yada labaran da yunkurin matsa lamba ba gaira-ba dalili domin wasu da zasu zabi Paparoma su ki yin zaben a watan gobe.