Mutum guda ya rasa ransa a Wukari

Rahotanni daga jihar Taraba a Najeriya na cewa tashin hankali ya barke a garin Wukari inda aka samu kone-kone da kuma jikkatar mutane da dama.

Tashin hankalin dai ya barke ne da safiyar yau.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani game da musababbin tashin hankalin amma wasu mazauna garin sun gaya mani cewa lamarin na da nasaba da amfani da wani filin kwallo tsakanin gungun-gungun matasa dake kwallon kafa, a unguwar Tsohuwa Mayaka, kuma kasancewar bangarorin biyu sun fito ne daga addinai da kuma kabilu mabambanta, sai lamarin ya rikide ya zamo na addini.

Ganau dai sun ce nan take mutum guda ya rasa ransa, daga nan kuma sai matasa suka kama kone-konen gidaje da wuraren kasuwaci da na ibada, kuma harkoki a cikin garin suka tsaya cik.

Wani mazaunin garin da ya bukaci kada in ambacin sunansa, ya shaida mani cewa ya tabbatar da mutuwar mutne uku yayin da wasu da dama kuma suka jikkata, inda kuma ake ta harbe-harben bindiga.

Dana tuntubi kakakin rundunar yan sandan jihar ta Taraba, DSP Amos Olaoye, ya tabbatar mani da faruwar tashin hankalin, amma ya ce kawo yanzu bai samu cikakkken bayani ba tukuna daga jami’ansu dake yankin.

Jihar ta Taraba dai na daya daga cikin jihohi da suka fi gamin gambizar al’umomi inda a wasu lokutan ake samun sabani a tsakaninsu.