An kai hari kan masu jana'iza a Kaduna

A jihar Kaduna dake arewacin Najeriya wasu da ba a san ko su wanene ba sun kai wani mummunan hari a garin Adduwan Gida dake karamar hukumar Zangon Kataf.

Rahotanni dai na cewa, an hallaka kimanin mutane shida yayin da wasu mutanen goma suka samu munanan raunuka.

Rundunar 'yan sandan jahar ta Kaduna ta tabbatar da afkuwar lamarin kuma ta ce zata tura mutananta wajan, domin gano ainahin abin da ya faru. tare da tabbatar da kwanciyar hankali.

Tun bayan zaban shugaban kasar da akai ne dai a kasar ake ta samun kai hare hare a kudancin Kaduna, wanda wasu ke dangantawa da ramuwar gayya.

Karin bayani