An nuna bidiyon 'Faransawan da aka sace'

Faransawa
Image caption Faransa ta ce wannan hoton abin tayar da hankali ne

Wani hoton bidiyo da aka sa a shafin internet na You Tube ya nuna iyalan Faransawan nan bakwai, ciki harda 'ya'yansu da wasu 'yan bindiga suka sace a Kamaru.

Hoton bidiyon ya nuna wani mutum yana karanta jawabi a gaban maza biyu da mace daya da kuma yara hudu.

Mutanen da suka ce su 'ya'yan Jama'atu Ahlus sunna liddaa'awati wal jahad da aka fi sani da Boko Haram ne, sun nemi a saki fursunonin da ake tsare da su a Najeriya da kuma Kamaru.

Iyalan dai na zaune ne a birnin Yaounde na kasar Kamaru, inda mahaifinsu ke aiki da kamfanin gas na Faransa Suez. An sace su ne lokacin da suke komawa gida daga wurin shakatawa ba Waza National Park.

Mutumin da ke jawabi a bidiyon, ya ce "muna gaya wa shugaban Faransa cewa mu 'yan kungiyar Boko Haram ne muka kame iyalan Faransawan su bakwai".

'Matukar kaduwa'

Kungiyar ta yi barazanar za ta kashe Faransawan matukar ba a biya masu wasu bukatun su ba, da suka hada da sako wasu 'yan kungiyar da ake rike da su a gidajen kason Najeriya da Kamaru.

Sun kuma zargi shugaban Faransa Francois Hollande, da kaddamar da yaki a kan Musulunci, abin da ke nuni da yakin da dakarun Faransa ke yi a kasar Mali.

A ranar Alhamis Faransa ta ce tana da masaniyyar cewa "kungiyar Boko Haram ce ta sace mutanen", kuma an shiga da su Najeriya daga Kamarun.

"Wannan hoton abin tayar da hankali ne, kuma mun yi matukar kaduwa," a cewar ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius, cikin sanarwar da ya fitar.

A makon da ya gabata ne dai wasu mutane akan babura suka sace iyalin Faransawan.

Turawan dai a cikin bidiyon, sun nuna cewa suna cikin koshin lafiya, babu kuma wata alamar tagayyara tare dasu. Wani na kusa da su ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP cewa hoton na hakika ne.

An yi dai ta samun rahotanni masu karo da juna tun daga wancan lokaci game da makomar mutanen da kuma yunkurin da ake na ceto su.

Karin bayani