Jirgin balan-balan ya kashe mutane a Masar

Jirgin balan-balan
Image caption Kusan dukkan wadanda suka mutu 'yan yawon bude ido ne

'Yan kasashen waje 19 ne ciki harda Burtaniya da Faransa da Hong Kong, suka mutu a lokacin da jirgin balan-balan na 'yan yawon bude ido ya yi hadari a birnin Luxor na kasar Masar.

Balan-balan din tana sama ne da mita 300 lokacin da ta kama da wuta sannan ta fadi a wani fili da ke yammacin Luxor, a cewar hukumomi.

Akalla mutane biyu ne ciki harda matukin balan-balan din, aka bayar da rahoton sun rasa rayukansu; bayan da suka fice daga ciki kafin ta fadi.

Birnin Luxor na daya daga cikin biranen Masar da ke da kayayyakin tarihi da suka fi yin fice.

Yana kusa da kogin Nile na Kudancin kasar, kuma yana da matukar farin jini ga 'yan yawon bude ido.

Hadarin ya faru ne a daya daga cikin wurin da aka fi amfani da shi wajen hawa jirgin balan-balan din, wanda ke baiwa 'yan yawon bude ido damar ganin wuraren tarihi na birnin na Luxor.

'Yan sandan kasar Masar sun ce wadanda lamarin ya ritsa da su sun hada da mutane tara daga Hong Kong, hudu daga Japan, biyu daga Burtaniya, biyu daga Faransa da kuma biyu daga Masar.

Karin bayani