Rantsar da Park Geun-hye a Korea ta Kudu

sabuwar shugabar kasar Korea ta kudu Park Geun-hye
Image caption An rantsar da Park Geun-hye a gaban dubun dubatar mutanen Korea ta Kudu

Mace ta farko da aka zaba a matsayin shugabar kasar Korea ta Kudu, Park Geun-hye, ta sha rantsuwar kama aiki yayin wani biki a Seoul, babban birnin kasar.

A jawabinta ga dubun dubatar mutanen da suka halarci bikin, Shugaba Park ta yi kira ga Korea ta Arewa ta yi watsi da burinta na mallakar makamin nukiliya.

Ta kwatanta gwajin nukiliya na uku da Pyongyang ta yi kasa da makwanni biyu da suka wuce da cewa kalubale ne ga dorewar al'ummar Korea.

Ta kara da cewa Korea ta kudu ba za ta amince halin da ake ciki a yanzu ya cigaba ba.

A dan haka kofa a bude take ga Korea ta kudu ta tabbatar da yarda da juna,ta hanyar hawa teburin shawarwari a kan alkawuran da aka riga aka yi tuntuni.

Shirin tabbatar da yarda da juna tsakanin kasashen biyu na daga cikin muhimman batutuwan da Ms Park ta yi amfani da su yayin kamfe din ta.

Sai dai a halin yanzu ba kalubalen matsalar tsaro kadai za ta fuskanta ba,domin tattalin arzikin Korea ta kudu ya yi kasa,yayin da yawan al'umar kasar ke karuwa,sannan duka bangarorin siyasar kasar ke bukatar ludayin arzikin kasar ya kewaya.