'Jarirai na gane magana tun suna ciki'

Jariri
Image caption Jarirai na iya bambanta muryoyin maza da mata tun suna ciki

Wadansu masana kimiyya a kasar Faransa sun ce jariran da ke cikin mahaifiyarsu na iya fahimtar sautin magana watanni uku kafin a haife su.

Ta hanyar amfani da na'urar daukar hoton ciki yayin da ya kai makwanni ashirin da takwas, kungiyar masanan daga Jami'ar Picardie ta kasar ta Faransa ta bayyana cewa tun a ciki jariran na iya banmbancewa tsakanin muryoyin maza da na mata.

Tuni dai masu binciken kimiyya sun sun cewa jarirai a cikin mahaifiya na iya jin sauti a lokacin da kaifin jinsu ya fara bunkasa a makwanni ashirin da uku kafin a haifesu.

Masanan na Faransa sun ce a yanzu sun yarda cewa kwakwalwar dan-Adam na da wata baiwa daga Allah ta fahimtar magana.

Karin bayani