Blair: Kawar da Saddam ya fi barinsa

Tony Blair
Image caption Tsohon Firayim Ministan Burtaniya Tony Blair ya amnice mutanen Iraki na shan wahala

Tsohon Firayim Ministan Burtaniya Tony Blair ya amince cewa rayuwa a kasar Iraki har yanzu ba ta kasance yadda ya yi hasashen za ta kasance ba shekaru goma da suka gabata, lokacin da ya yi kawance da Amurka wajen afkawa kasar da yaki.

A wata tattaunawa da ya yi da BBC yayin da da ake cika shekaru goma da afkawa Iraki da yaki, Mista Blair ya ce duk da cewa an samu ci gaba har yanzu mutane na rayuwa cikin kunci sakamakon yake-yaken da ake ci gaba da yi.

“Ga wadansu mutane a Iraki rayuwa na da matukar wahala, musamman idan mutum yana zaune a Bagadaza—babban birnin kasar—da tsakiyar kasar; har yaznu ana samun ayyukan ta'addanci wadanda ke haifar da salwantar rayukan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, amma a kasar baki daya tatalin arziki na kara bunkasa”, inji Mista Blair, wanda ya kara da cewa: “Amma na yarda cewa har yanzu akwai matsala”.

A karamin takadiri dai an kiyasta cewa zuwa shekarar 2003 dubban daruruwan fararen hula sun rasa rayukansu; sojojin Burtaniya 179 kuma sun mutu.

Da aka tambaye shi ko bay a ganin wannan asarar ta yi yawa, sai ya ce:

“Babu shakka asara ce mai matukar yawa, amma kuma a dubi irin kudar da mutane ke dandanawa kafin a tumbuke gwamnatin Saddam [Hussain].

“Dubi yakin Iran da Iraki, wanda ya haddasa mutuwa ko jikkatar mutane miliyan daya. An kashe dubban daruruwan sojojin Iran—akasari ta hanyar amfani da makamai masu guba.

“[Saddam Hussain] ya kuma yi amfani da makami mai guba a kan mutanensa Kurdawa. A kullum ana kashe mutane, ana gana musu ukuba.

“Saboda haka ba mafita ba ita ce a shaidawa mutane cewa da an bar Saddam tunda da yana nan masu tayar da kayar baya ba za su shiga kasar su yi yukunrin hargitsa tab a; ina ganin mafita ita ce a tumbuke mai mulkin kama-karya in ya so daga baya a san yadda za a yi a yi waje da masu tayar da kayar bayan”.

Karin bayani