Majalisar Amurka ta amince da nadin Hagel

Chuck Hagel
Image caption Bayan kai ruwa rana, Majalisar Dattijan Amurka ta amince da nadin Chuck Hagel

Majalisar Dattijai ta Amurka ta tabbatar da nadin tsohon dan majalisar na jam'iyyar Republican, Chuck Hagel, a matsayin sabon sakataren tsaron Shugaba Obama.

A birnin Washington dai ba kasafai abubuwa kan tafi yadda ya kamata ba, sannan kiki-kaka ba wani bakon abu ba ne, amma a karshe batun nadin Mista Hagel din ya zama tarihi.

Sakamakon kuri'ar da aka kada a ya nuna cewa har kwanan gobe Mista Hagel ba shi da farin jini a wajen tsofaffin abokan aikinsa ’yan jam'iyyar Republican.

Yayin wani zama a watan Janairu don sauraren bahasi kafin amincewa da nadin nasa, Mista Hagel, wanda tsohon sojan Amurka ne da ya yi yakin Vietnam, kuma tsohon dan Majalisar Dattijan daga Nebraska, ya sha binciken kwakwa.

Ya fuskanci tsauraran tambayoyi a kan yadda ya kan saki jiki ya yi magana a kan Iran, da ra'ayinsa dangane da abin da ya taba kira ‘kasafin kudin Ma'aikatar Tsaro ta Pentagon na garari’, da kuma zargin cewa ya tsani Isra'ila da magoya bayanta na Washington.

Kuma amsoshin da ya bayar ba su kayatar ba, har ma wadansu daga cikin masu tsananin adawa da Barack Obama suka hango wata dama da a lokaci guda za su hana tabbatar da Mista Hagel su kuma kunyata shugaban kasar.

Amma fa duk da yunkurin da aka jima ana yi na hana kada kuri'a a kan cancantar Mista Hagel, fadar gwamnati ta White House ta tsaya kai-da-fata har sai da a karshe ’yan jam'iyyar ta Republican suka ga cewa ba sarki sai Allah suka saduda.

A yanzu dai Mista Obama ya samu sakataren tsaron da ya ke so, amma fa Mista Hagel yana da aiki a gabansa.

Ranar Juma'a zai fuskanci wani kalubale na gaggawa: wato yadda zai bullowa ragin biliyoyin dalolin da ’yan majalisar wakilai suka yi a kasafin kudin Ma'aikatar Tsaro ta Pentagon wanda ka iya haifar mata da mummunan sakamako.

Karin bayani