Kiki-kaka a kan zaben kasar Italiya

Shugabannin jam'iyyun siyasar Italiya
Image caption Shugabannin jam'iyyun siyasar Italiya

Shugaban Jama'iyar masu matsakaicin ra'ayin sauyi a Italiya ya bayyana kiki- kakar da ta biyo bayan babban zaben kasar a matsayin wani abun mamaki.

Pier Luigi Bersani -- wanda kawancensa ya lashe galibin kujeru a majalisar dokoki -- ya ce yana sane da haduran da matsalar siyasa ta haddasa, abinda ya fito fili a faduwar darajar kasuwannin hannayen jari da kuma ta kudin Euro.

Mr Bersani ya ce zai yi kokarin amsa bukatun jama'a na neman sauyi, to amma ya kalubalanci shugaban Jama'iyar nunin rashin jin dadi da inda Italiyar ta dosa, Beppe Grillo domin zayyana shirinsa ga Italiya.

Inda ya ce, sun yi kokarin mayar da martani , to amma dole ne ya amsa cewar matsalar tafi karfinsu.

A halin yanzu suna bukatar amsar abunda ya fito daga zaben nan tare da karfin hali, sannan su tabbatar da kudurinsu ta yadda zai amfani kasar.

Mr Bersani ya gabatar da wani takaitaccen shiri , amma har yanzu babu tabbas a kan ko ya Alla zai iya kafa wata gwamnati.

Karin bayani