'Sojin Ivory Coast na azabtar da mutane'

Shugaba Alassane Ouattara na Ivory Coast
Image caption Shugaba Alassane Ouattara na Ivory Coast

Wani rahoto da kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ta fitar yau ya ce batutuwan da suka shafi take hakkin bil-Adama a wurare da dama inda dakarun kasar Ivory Coast ke farautar magoya bayan tsohon Shugaba Laurent Gbagbo na kawo tarnaki ga shirin sulhu.

A watanni shidan da suka gabata, kungiyar ta tattara bayanan da ke nuna cewa rundunar sojin kasar wadda Shugaba Alassane Ouattara ya kafa tana ganawa mutane ukuba, tana kisan mutane ba tare da yi musu shari'a ba da kuma kama su babu gaira babu dalili.

Manufar kafa rundunar dai ita ce shigar da dakarun da ke biyayya ga tsohon shugaban kasar, Laurent Gbagbo, cikin sojin kasar bayan tashin-tashinar da ta biyo bayan zaben 2010.

Rahoton ya ce sojoji, da ma sojojin sa-kai, na cin karensu ba babbaka.

Kungiyar ta Amnesty ta kuma nemi a kafa wani kwamitin kasa-da-kasa domin bincikar kisan da aka yi wa mutane goma sha hudu a yammacin kasar, bisa zargin cewa su magoya bayan Mista Gbagbo ne.

Karin bayani