Ba adalci a tsarin harajin Italiya - Maradona

Diego Maradona
Image caption Har yanzu magoya bayan Napoli suna ganin kimar Maradona

Shahararren dan kwallon Argentina Diego Maradona ya nemi mahukunta a Italiya su yi masa 'adalci' a takaddamar harajin da suka dade suna yi.

Da yake magana a birnin Naples na kasar ta Italiya, ya nemi ya tattauna maganar da shugaban kasar Giorgio Napolitano.

An nemi tsohon dan wasan na Argentina da Napoli ya biya Yuro miliyan 37 (dala miliyan 48) na kudaden harajin da bai biya ba a shekara ta 2005.

Maradona, mai shekaru 52, ya taka leda a Kulob din Napoli tsakanin shekarun 1984 da 1991, inda ya taimaka musu suka lashe gasar Serie A sau biyu.

"....ni zan biya ba su ba?"

Ya nanata cewa wasu kusoshin kulob din na lokacin ke da alhakin lamarin.

"Mai yasa za a ce ni zan biya ba su ba?" kamar yadda ya ce a wani taron manema labarai tare da lauyoyinsa da kuma masu kare lafiyarsa.

"Na samu kaina a wannan halin ne saboda na samu kudade da yawa amma ban san komai ba game da batun kwantiragi.

"Ban kashe kowa ba. Na zo nan ne domin neman a yi min adalci."

Karin bayani