An kashe kwamandan 'yan sanda a Najeriya

Marigayi Dahiru Musa Majiya
Image caption Ranar Litinin da dare wasu 'yan bidiga suka harbe Dahiru Musa Majiya a gidansa da ke Kano

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano a arewacin Najeriya ta tabbatar da kashe wani babban jami’inta da wadansu ’yan bindiga suka harbe a daren ranar Litinin.

Rundunar ta ce an kashe Dahiru Musa Majiya ne a gidansa dake unguwar Sabuwar Gandu.

Marigayin dai shi ne kwamandan ’yan sandan kwantar da tarzoma na jihar Kano.

Marigayin dai dan uwa ne ga kakakin rundunar ’yan sandan Jihar ta Kano, Magaji Musa Majiya.

A baya ma dai an sha kai hare-hare a kan jami’an tsaro a arewacin Najeriya—hare-haren da ake dangantawa da kungiyar Jama’atu Ahlis Sunnah lid Da’awati wal Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram.

Manazarta dai na cewa wannan kisan na nuni da cewa idan har za a harbe babban jami’in tsaro a Najeriya har Lahira, to farar hula kuma dab a shi da makamin kare kansa ya zai yi ke nan?

Karin bayani