Birtaniya ta gargadi 'yan kasarta a Najeriya

Ministan harkokin wajen Birtaniya
Image caption Ministan harkokin wajen Birtaniya

Gwamnatin Birtaniya ta gargadi 'yan kasarta dake zaune a Najeriya, da su guji zuwa wasu jihohi a arewacin Najeriya, biyo bayan karuwar hare-hare da sace mutane a yankin.

Shawarar hana tafiye-tafiyen, wadda aka wallafa a shafin intanet na ofishin jakadancin Birtaniya a Najeriya, ya ce a yanzu yankunan da take shawartar 'yan kasarta su kauce wa kwata-kwata, sun hada da jihar Bauchi da garin Okene na jihar Kogi.

Sauran jihohin da biranen sun hada da Borno da Yobe, da Delta da Bayelsa, da Rivers da kuma Akwa Ibom.

Haka kuma sanarwar ta gardadi 'yan Birtaniya da kada su je biranen, Kano da kuma Warri.

Yayin da kuma Birtaniyar ta ce idan ba tafiyar da ta zama dole ba, kada 'yan kasar su je duk wani yanki dake jihar Kaduna da Kano da Jigawa da Katsina da Gombe da kuma biranen Jos da Riyom da kuma Barikin Ladi a jihar Plato.

Sace-sacen 'yan kasashen waje dai ya karu a arewacin kasar a baya-bayan nan, inda a jihar Bauchi aka sace wasu turawa ma'aikatan kamfanin gine-gine na Setraco ciki har da dan Birtaniya.

Yayin da kawo yanzu babu labarin wani Bafaranshe da aka sace a jihar Katsina, sannan ga Faransawa bakwai da kungiyar nan ta Jama'atu Ahlul Sunna lil da'awati wal jihad ko Boko Haram ta kame a kasar Kamaru kuma take garkuwa da su.

Haka kuma a kudancin kasar, yankin da sace mutane da yin garkuwa da su, ba sabon abu bane, rahotanni sun ce an saki wasu 'yan kasar waje bakwai ma'aikatan jirgin ruwan da aka yi garkuwa da su a jihar Bayelsa.