Hari kan makwancin 'yan kasashen waje a Najeriya

Nigeria
Image caption Ana kaiwa 'yan kasashen waje hari a baya-bayan nan a Najeriya

Akalla jami'an tsaro biyu ne aka kashe lokacin da wasu 'yan bindiga sun kai hari a gidan kwanan wasu ma'aikatan kamfanin gine-gine na kasar Lebanon a garin Tella na jihar Taraba a Najeriya, a cewar rahotanni.

Jami'an tsaro a jihar sun tabbatar da afkuwar lamarin, wanda ya jikkata wani ma'aikacin kamfanin na Triacta, amma ba su yi karin haske ba.

Wakilin BBC a Arewa maso gabashin Najeriya Is'haq Khalid, yace 'yan kasashen waje da ke zaune a gidan sun tsira ba tare da ko kwarzane ba.

Yanzu haka ma dai ana ci gaba da laluben wasu 'yan kasashen wajen su bakwai ma'aikatan kamfanin gine-gine na Setraco da Jama'atu Ansarul Musulumina Fibiladis Sudan ta yi ikirarin kama su saboda abin da ta kira zaluncin kasashen yamma ga musulmi kamar a Mali da Afghanistan.

Bayanai dai na cewa 'yan bindigar da ba a san ko su wanene ba sun yi dirar mikiya ne ga gidan na kwanan ma'aikatan kamfanin gine-gine mallakin 'yan kasar Lebanon da misalin karfe tara na daren ranar Laraba.

A garin Mutum biyu ma...

Maharan sun bude wuta ga mutanen da ke mashigar gidan sannan suka yi awon gaba da bindigogin jami'an tsaro da ke aiki a wajen.

"'Yan sanda biyu aka kashe kana aka jikkata wani injiniya na kamfanin", a cewar malam Tanimu Danjuma da ke aiki da 'yan kasar ta Lebanon a kamfanin Triacta.

Wannan lamari na garin Tella dai na zuwa kasa da sa'o'i 48 da wasu 'yan bindigar suka kashe 'yan sanda biyu a garin Mutum Biyu hedikwatar karamar hukumar ta Gassol.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Taraba DSP Mos Olaoye, ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin amma ya ce ba a yi masa cikakken bayani a hukumance ba.

Kawo yanzu dai ba a san ko su wane ne suka kai harin ba kuma ba a tabbatar ko 'yan kasashen wajen ne 'yan bindigar suka yi hako ba, amma dai a baya-bayan nan yan kasashen waje na yawan fuskantar barazanar kamawa da kuma kashewa daga 'yan bindiga a Najeriya.

Karin bayani