Dennis Tito na shirin zuwa duniyar Mars

Dennis Tito
Image caption Dennis Tito

Biloniyan Amurkan nan, kuma dan yawon bude ido a tashar binciken sararin samaniya na farko a duniya, Dennis Tito ya bayyana cewar zai dauki nauyin wani yunkurin zuwa duniyar Mars a 2018.

A wannan shekarar ne duniyar Mars din za ta karaci duniya sosai, to amma har a haka tafiyar za ta dauki kwana 500.

Mr Tito ya ce yana neman namiji da mace masu matsakaitan shekaru domin aikinsa na karfafa guiwar zuwa duniya Mars.

Ya ce kunbon ba zai sauka a kan duniyar Mars din ba, amma zai yi shawagi da nisan mil dari daga gare ta, sannan ya dawo duniya.

Mr Tito ya ce yayi amannar yunkurin ya wajaba domin kyautata gogewa da ilmin bil adama, amma kuma ya amince da irin haduran lafiya da kuma na tunani da tawagar maziyartan za ta fuskanta.