Za a takaita garabasar bankuna a Turai

Bankin Kungiyar Tarayyar Turai
Image caption Bankin Kungiyar Tarayyar Turai

Masu bankuna a kungiyar Gamayyar Turai za su samu kansu cikin shirin takaita garabasar da ake bai wa masu hannun jari daga shekara mai zuwa.

Wannan ya biyo bayan sakamakon yarjejeniyar da aka cimma a birnin Brussels.

Yarjejeniyar wadda 'yan majalisar kungiyar kasashen Turai ta EU, da wakilan gwamnatoci da jami'ai suka cimma, na daga matakan da aka tsara aiwatar wa domin kare sake aukuwar matsalar durkushewar bankuna.

A karkashin wannan shiri dai za a tsara yawan garabasar da za a bayar ne dai dai da kimar albashin shekara.

Sai dai za a iya kara yawansa amma za a iya yin hakan ne da izinin masu hannun jari kawai.

Bayar da garabasa mai yawan gaske dai ita ake ganin ta haifar da galibin matakan da suka haifar da matsalar tattalin arziki ta 2008,ta kuma kasance tamkar guba ga harkokin siyasa ta yadda ya kai ga tilasta amfani da kudaden gwamnati domin biyan basukan bankunan da suka durkushe.

Wannan mataki dai, wanda wajibi ne mafi yawan kasashen Kungiyar Gamayyar Turai su amince da shi, ana ganin wata galaba ce a kan Birtaniya wadda ita ce babbar matattarar cibiyoyin harkokin kudade a Turai.

Domin tuni daman masu bankuna a birnin Landan suka nuna korafinsu da fargaba a kan tsarin, inda suka ce matakin zai sa a karkatar da harkokin kasuwanci zuwa kasashen da suke wajen kungiyar Gamayyar Turai.