Paparoma Benedict ya bar fadar Vatican

Paparoma Bernedict
Image caption Tuni Paparoma Bernedict ya isa masaukinsa da ke Castel Gandolfo

Paparoma Benedict XVI ya bar fadar Vatican a rana ta karshe da yake barin mukaminsa na shugabancin darikar Katolika.

Tsohon dan shekaru 58, an dauke shi ta jirgin helikwafta zuwa wurin da zai kebe kansa a Castel Gandolfo, kusa da birnin Rome.

Da misalin karfe 7 agogon GMT wato 8 agogon Najeriya ne zai bar mukamin Paparoma baki daya.

Mataimakinsa Cardinal Tarcisio Bertone, shi ne zai karbi ragamar na wucin gadi har zuwa lokacin da za a zabi sabon Paparoma a watan gobe.

Kimanin mutane biliyan daya da miliyan 200 ne magoya bayan darikar Katolika a duniya.

Tun da farko Paparoma Benedict ya gana da manyan Cardinal-cardinal na cocin, inda ya yi alkawarin 'biyayya da goyon baya' ga wanda zai gaje shi.

Nan da 'yan kwanaki masu zuwa ne, Cardinal din kimanin 115 daga sassa daban-daban na duniya, kuma 11 daga cikinsu sun fito daga nahiyar Afirka, zasu kulle kansu a Vatican, inda za su kada kuri'ar zaben sabon Paparoma.

Zaben dai na iya daukar kwanaki ko makonni.