Bama-bamai sun tashi a Maiduguri

A Najeriya rahotanni daga Maiduguri babban birnin jihar Borno da ke arewacin kasar na cewa an samu tashin wasu bammabamai a cikin unguwani biyu , inda kuma suka halaka wasu jami'an tsaro .

Lamarin dai ya faru ne a unguwannin kwastan na Bolori, inda ya hallaka sojoji biyu da kuma fararan hula da dama.

Wannan tashin bommabomai ya faru ne a daidai lokacin da ake gudanar da taron gwamnonin jam 'iyun adawa da ke kokarin girka babbar jam'iyar adawa ta APC wato All Progressive Congres.

Har yanzu dai ba wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin tada bama-baman.