Paparoma Bernedict zai bar fadar Vatican

Paparoma Bernedict
Image caption Paparoma Bernedict

Yau Paparoma Bernedict ke shirin barin fadar Vatican, bayan yayi murabus daga mukaminsa na shugaban Cocin Roman Kotolika na duniya.

A ranar Laraba ne dubun dubatar jama'a suka hallara a dandalin St. Peter a birnin Roma, inda Paparoman ya yi bayyanar sa ta karshe, yanzu kuma hankali ya karkarta wajen zaben sabon paparoman da zai maye gurbinsa.

Paparoma na goma sha shida zai tashi ne ta jirgi mai saukar angulu da misalin karfe biyar na yamma agogon Najeriya daga fadar Vatican, zuwa wani wuri mai nisan mil goma sha biyar a kudu maso gabashin birnin Roma.

A can ne zai zauna har wajen karshen watan Aprilu ya zuwa farkon watan Mayu, lokacin da zai koma fadar ta Vatikan, bayan an gama gyara masa wurin da zai zauna a kebe.

Kafin ya tashi a yau din zai yi ban kwana da shugabannin Cocin na Katolika masu mukamin Cardinal, wadanda tuni suka isa birnin Roma domin shirin zaben sabon Paparoma.

Daga karfe takwas na daren yau ne kujerar Paparoman za ta kasance babu kowa a kan ta.

Wani kwamiti ne na Cardinal zai tafiyar da al'amuran Cocin na wucin gadi, daga nan ne zasu shiga batun zaben sabon Paparoma.

Nan da 'yan kwanaki masu zuwa ne, Cardinal din kimanin 115 daga sassa daban-daban na duniya, kuma 11 daga cikinsu sun fito daga nahiyar Afirka, zasu kulle kansu a Vatikan, inda zasu kada kuri'ar zaben sabon Paparoma.

Zaben dai na iya daukar kwanaki ko makonni.